<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>238</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, Ubangijinmu,
 Muna roƙon taimako,
 Ga mu nan, mu marasa ƙarfi,
 Sai ka shigo wurinmu.

[V2]
 KORUS
 Zo yanzu, cika mu,
 Yesu muna roƙonka.
 Cika mu da naka iko,
 Ba mu ƙarfin zuciya,

[V3]
 2) Ga mu nan a gaban kursiyin,
 Muna jiran ikonka.
 Ban da kai, ya Ubangiji,
 Ba mu iya kome ba.
 Korus

[V4]
 3) Ƴanuwanmu cikin duniya,
 Ga su suna mutuwa.
 Suna zaune cikin duhu,
 Ba su san tafarki ba.
 Korus

[V5]
 4) Ubangiji, muna roƙo,
 Cika mu da ƙaunarka.
 Bari Ruhunka ya ja mu,
 Har mu cika aikinka.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Yesu, Ubangijinmu, Muna Roƙon Taimako LW238</title>
</song>